An sami rahoton barkewar kazamin fada a garin Bama da ke arewa maso gabashin Nijeriya, inda sojoji su ka yi kokarin hana 'yan bindigar Boko Haram kai hari.
Shaidu sun ce daruruwan 'yan bindiga cinkushe cikin motocin daukar kaya da na yaki, sun danna zuwa garin da safiyar yau Litini, to amma sai sojojin Nijeriya da ke wani barikin soja na yankin su ka tinkare su.
Wani jami'in tsaro da ke wurin mai suna Muhammad Gava, ya shaida ma Muryar cewa da farko sojojin sun fatattaki 'yan bindigar, to amma sai su ka sake damara su ka kawo hari. Zuwa karfe sha biyun rana babu cikakken bayani kan ko 'yan Boko haram din sun yi nasarar kwace garin, mai tazarar kilomita 70 daga Maiduguri, hedikwatar jihar.
Kafafun soji da su ka yi ma 'yan jarida jawabi a birnin Maiduguri sun ce an raunata 'yan bindiga 30, yayin da aka kuma kashe 70. Nan take dai ba a san adadin sojojin da abin ya rutsa da su ba.
Wannan shine babban hari na uku da 'yan Boko Haram su ka kai kan Bama, bayan harin da su ka kai cikin watan Mayun 2013 da kuma Fabrairun wannan shekarar.
Cikin makonnin baya-bayan nan, wannan kungiyar ta kwace wasu sassan jihar Borno, ciki har da garin Gwoza, wanda ya shiga abinda Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya kira "Daular Islama."