Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Tashi A Birnin Nairobi A Kenya Ya Kashe Mutane Akalla Biyu

Kayayyakin fasinjoji suke watse kusa da wata motar kiya kiya bayan da bam ya tashi a birnin Nairobi,lkacinnda motar take lodin zuwa Kampla.

‘Yansanda a Kenya sunce bam da aka boye cikin wata jaka ya tashi kusa da wata motar kiya-kiya jiya litinin a birnin Nairobi,ya kashe akalla mutane biyu,da jikkata wasu 26.

‘Yansanda a Kenya sunce bam da aka boye cikin wata jaka ya tashi kusa da wata motar kiya-kiya jiya litinin a birnin Nairobi,ya kashe akalla mutane biyu,da jikkata wasu 26.

Jami’ai suka ce bam din ya tashi ne dab da mutane sun fara shiga motar dake haramar tashi zuwa Kampala,fadar kasar Uganda.

‘Yansanda suka ce fasinjan dake dauke da jakar dake kunshe da bam din ya ankara cewa ‘yansanda suna duba kayan fasinjoji sai ya yada jakar ya yi kokarin gudu. Yana daga cikin wadanda bam din ya kashe.

XS
SM
MD
LG