A dalilin bom da ya tashi a babbar kasuwa jihar Bauchi mun samu zantawa da kakakin rundunar ‘yan sanda DSP Haruna Muhammad, wanda yayi muna karin haske. Yace wannan tashin bom in yayi sanadiyar mutuwar mutane bakwai (7) wanda kuma ishirin da biyar (25) suka jikkata, wanda yanzu haka ma mutun shida har sun murmure ankuma sallame su daga asibiti, mutane shatara na nan kwance a asibiti don karbar magani.
A cewar shikuma kakakin rundunar ‘yansandar jihar Gombe, DSP Fajir Attajiri, ya fara da yima al’umah jaje, wanda yace wannan ba'a bun jindadi bane saboda an rasa rayukan mutane goma shatara wasukuma da dama sunji rauni. Yakuma ba ma al’umah shawara cewar ganin wannan lokacin bukin kirismas ne da kuma karshen shekara, don haka mutane suyi taka tsan-tsan da yadda suke tafiyar da al’amuransu kuma idan suka ga wani abu da basu gamsu dashi ba to su hanzarta su sanar da hukuma, ya kara da cewar aikin tsaro bana sune kawai ba na kowa da kowa ne. A cewar wani mai sharhi a kan tsaro Dr. Bawa Wase, yace matakan tsaro da ake dauka, a tshar moto, asibitoci, da kasuwanni, bai kamata ace ana daukar matakai na rabi da rabi ba, matakaine da yakamata a daukesu da matukar mahimanci. Ya kuma kara da cewar duk wata mota da zata shiga wadannan wuraren to yakamata a sa abun tantancewa don ganin me ke cikin motar, haka suma wadanda ke shiga da jakunkunan su yakamata a dubasu babu babba babu yaro.