Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin mutane dubu daya ke kamuwa da kwayar cutar HIV kowacce rana a Najeriya


Wata mace tana amfani da sabon abin gwada cutar HIV
Wata mace tana amfani da sabon abin gwada cutar HIV
Kwararru a fannin aikin jinya sun yi kiyasin cewa, kimanin mutane dubu daya suke kamuwa da kwayar cutar HIV kowacce rana a Najeriya.

Datekta janar na cibiyar yaki da cutar kanjamau na kasa Frofesa John Idoko ne ya bayyana haka a wajen wani taron yaki da cutar kanjamau na kasa da kasa da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

Frofesa Idoko yace, ganin yadda wannan cutar ke ci gaba da yaduwa, ya sa gwamnatin Najeriya ta kuduri aniyar daukar dukan wani mataki na kasa da kasa da suka kamata domin shawo kan yada ta.

Bisa ga cewarshi, taron da kasa da kasa da aka gudanar a birnin Washington kan yaki da cutar kanjamau ya kara bude masu ido kan ingancin sababbin magungunan yaki rage kaifin cutar a duniya baki daya.

Ya kuma bayyana damuwa sabili da bisa ga cewarshi, karancin kudi yana gurguntar da yunkurin rage yada kwayar cutar HIV daga uwa zuwa jariri musamman a wannan lokacin da kasashen da ke bada tallafi suke rage kudin da suka badawa.

Darektan cibiyar yaki da cutar kanjamau ya kuma bayyana cewa, Najeriya tana samar da kimanin kashi ishirin da biyar bisa dari ne kawai na kudin da ake kashewa a yaki da cutar kanjamau, yayinda sauran kudin yake fitowa daga kungiyoyi da gwamnatocin kasashen waje.

A halin yanzu dai Najeriya tana matsayi na biyu, bayan Afrika ta Kudu a cikin kasashen da suke da yawan wadanda ke dauke da kwayar cutar HIV.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG