Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Dubu Takwas Sun Rasa Gidajensu a Jihar Taraba


Wani yankin da ya fama da tashe-tashen hankula a arewa maso gabashin Najeriya
Wani yankin da ya fama da tashe-tashen hankula a arewa maso gabashin Najeriya

Kimanin mutane dubu takwas suka rasa muhallansu bayan wasu hare-hare da aka kai a kauyuka bakwai dake kananan hukumomin Lau, Ardo Kola da Yero dake jihar Taraba.

Mataimakin Gwamnan jihar Taraba, Haruna Manu ya jagoranci tawagar Gwamnatin jihar da ta sashen tsaro na kwamitin wanzar da zaman lafiya a Arewa maso gabashin Najeriya, don kai ziyarar gani da ido yankunan da abin ya shafa.

Mataimakin Gwamnan ya danganta lamarin da rashin hakuri da juna ya kuma kara da cewa Gwamnati na daukar matakin ganin cewa irin haka bai sake faruwa ba.

Hukumomi ba su bayyana wadanda suke da alhakin kai wannan hari ba, amma yankin jihar ta Taraba, yanki ne da ya ke yawan fama da rikicin makiyaya da manoma na tsawon wasu shekaru.

Halin da ake ciki yanzu a yankin ya jefa mazauna yankin cikin fargaba kamar yadda wani mazaunin yankin Danjuma Bako, ya ce matsallar rashin zaman lafiya shi ke jawo fargaba ya kuma kara da cewa jeka ka dawo suke yi da yara idan dare yayi domin kaisu ga mabuya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

XS
SM
MD
LG