WASHINGTON, DC —
Wata baiwar Allah Malama Hadiza Yusuf tace bata yarda ta zauna ba a ce komai sai mijinta yayi mata don wannan raguwar dubara ce. Ta kasance tana sana’o’I kamar kala hudu, kuma tana da ‘yaya uku kuma tana ganin ala dole mata su tashi su nemi na kansu kada suce sai abun da maigida yabada sannan za’ayi amfani da shi.
Wadannan sana’o’in na ta basu sa tazama wadda bazata iya aiwatar da duk wani abu da yakamata tayi a matsayinta na matar aure ba. Wannan ma wani karfin gwiwa yake bata. Sai dai tayi nuni da cewar matsalolin da suke samu shine ana karban kayan bashi kuma ba’a biya kan lokaci.