Addaidai lokacin da ya rake saura kwanaki biyar da cikar wa’adain shigar gasar nan ta Inganta Lafiyar Mata da Yara, mai suna 1 Million Health Innovation Challenge, wadda manufarta ita ce ceto rayukan mata da yara kanana kimanin miliyan guda kowace shekara, musamman ma a arewacin Najeriya, wani tsohon likitan Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) Dr Musa Soba, ya yi kira ga ‘yan Najeriya musamman ma ‘yan arewacin kasar, da su shiga wannan gasar gada-gadan.
Dr Soba ya ce alkaluma sun nuna cewa an fi samun mace-macen mata da matsa a arewacin Najeriya, saboda haka ya kamata kwararru daga yankin na arewa su fi kowa daka rawa a wannan gasar. Y aba ma don kyautar da ke tattare da gasar ba, ko ma don ‘yan arewar su nuna cewa sun san abin da ya kamata.
Kyautar gasar fasahar lafiya ta farko ta hada da $100,000; ta biyu ta hada da $50,000 sannan ta uku kuma $30,000.
Za a rufe gasar ranar 31 ga wannan wata na Maris. Za a iya aikawa da niyyar shiga gasar a www.nhim.phn.ng/competition
Hamshakan attajiran Najeriya, wadanda ke daukar nauyin gasar, ciki har da Alhaji Aliko Dangote da Mr. Jim Ovia; da kuma kwararru irinsu Dr. Muhammad Pate, da Mrs Joke Bakare da Ms Osas Ighodaro, su ma na kiran da a shiga gasar sosai.