Accessibility links

Kirista A Duk Fadin Duniya Sun YI Bukin Easter

  • Grace Alheri Abdu

Vatican Pope Easter
Kirista a duk fadin duniya suna bukukuwan Ista, rana mafi muhimmanci a addinin Kirista, da ake tunawa da tashin Yesu Almasihu daga matattu bayan kwana uku da giciye shi.

Sabon Paparoma da aka rantsar Pope Francis, shugaban darikar katolika na duniya, ya yi addu’oin Ista a dandalin St Peters.

Fadar Vertican tace kimanin mabiya darikar Katolika dubu dari biyu da hamsin ne suka halarci addu’oin. Jama’a sun yi ta sowa lokacin da aka zaga da Paparoman a cikin mota bayan addu’oin.
Daga baya Paparoma Francis ya yi jawabi daga barandar da ya fara gabatar da kansa bayanda zabe shi farkon wannan watan.

Ya yi kira da a zauna lafiya, musamman a wuraren da ake fama da tashe tashen hankali a kasashen duniya.
XS
SM
MD
LG