Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kisan Jama’a: Buhari Ya Gana Da Sufeto-Janar Na ‘Yan sandan Najeriya


Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya Idris Kpotun Ibrahim
Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya Idris Kpotun Ibrahim

Ganin yadda ake ta zub da jini a sassan Najeriya, Shugaban Najeriya ya kira Sufeton 'Yansandan kasar Idris Ibrahim a Fadarsa da ke Aso Rock, Abuja, inda ya yi ma Shugaban kasar yadda aka yi har ake ta karkashe jama'a a sassan kasar. Sufeto-Janar din dai ya kare matakan da ya dauka.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da Sufeto-Janar na ‘Yansandan Najeriya Ibrahim Idris saboda yawan kashe-kashen da ke faruwa da kuma wasu matsalolin tsaro a Najeriya musamman a jahohin Rivers Adamawa da Taraba da Kaduna da sauransu, inda kashe-kashen rashin imanin ya hada da mata da yaran da ba su ji ba ba su gani ba.

Bayan ganawarsa da Shugaba Buhari a Fadar Aso Rock kan wannan matsalar, Sufeto-Janar na ‘Yansandan Najeriya din ya bayyana ma ‘yan jarida cewa a duk lokacin da bukata ta taso, yakan yi amfani da rukunin ‘yansanda daidai bukatar ne. Ya ba da misali da matakin da ya dauka kan batun na jahar Binwai (Benue), inda ya ce baya ga Kwamishinan ‘Yansandan Jahar da Mataimakin Sufeto na ‘Yansandan wannan shiyyar ya kuma tura babban Mataimakinsa wata DIG saboda girmar matsalar.

A halin da ake ciki kuma, shi ma Ministan Cikin Gida Laftana-Janar Abdurrahman Bello Danbazau, ya je birnin Fatakwal na jahar Rivers, inda anan ma aka zubar da jini matuka. Da ya ke jawabi ga jama’a a jahar, Ministan ya ce Shugaban kasa fa ya kadu sosai da yadda ake ta kashe rayuka a sassan Najeriya; y ace don haka a yanzu ana nan ana nazarin yanayin tsaron baki daya.

Dakta Umar Ardo, wani tsohon malami a Jami’ar Soji ta NDA da ke Kaduna, inda nan ma aka yi kashe-kashe musamman ma a kudanci, ya ce Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanaji matakai da dama da za a iya mafani da su wajen shawo kan matsalolin tsaro don haka ya dora laifin kan Shugaban kasa, wanda y ace ya kasa amfani da wadannan matakan yadda ya kamata. To amma Sakatare-Janar na Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Mai Mala Boni, ya ce Shugaban kasa y aba da cikakken izini da umurni ga matakan tsaro kamar yadda ya kamata saboda tsai da duk wani tashin hankali.

Ga dai wakilinmu Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG