Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kisan Janar Idriss: Kotu Ta Ce a Cigaba Da Tsare Wasu Mutane 19


Wasu daga cikin masu sace mutane da kuma kisa a Najeriya
Wasu daga cikin masu sace mutane da kuma kisa a Najeriya

A wani al'amari mai nuni da sarkakkiya, da kuma girman laifin da ake tuhumar mutanen 19 nan da ake zargi kashe Janar Idriss Alkali (murabus), kotun da ke shari'ar laifin a Jos ta ba da umurnin a cigaba da tsare su, babu bale, har sai ranar da za a cigaba da sauraren karar wato 10 ga watan 12.

‘Yan kwanaki bayan jana’izar Janar Idriss Alkali, babbar kotu ta biyar da ke Jos, babban birnin jahar Filato, ta ba da umurnin a cigaba da tsare mutane 19 da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi ma tsohon janar din tare kuma da kokarin bad da sawu.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Daniel Longji, ya kuma dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Disamba, lokacin da za a cigaba zaman sauraren wannan shari’a mai cike da abubuwan tayar da hankali, da kuma nuni da irin matsalar tsaron da Najeriya ke fama da ita.

Rundunar ‘yan sandan jahar Filato ce ta maka mutane 19 din, ciki har da wata wace, wadanda ake zargi da hada baki a aikata ta’asa, da mallakar bindigogi da sauran muggan makamai na bisa ka’ida ba, uwa uba – da aikata kisan gilla ma Janar Idriss Alkali (murabus).

Ga wakiliyarmu ta Jos, Zainab Babaji, da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:19 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG