Panetta ya fadawa Muryar Amurka a ranar Alhamis cewa, idan har ta tabbata cewa Korea ta arewa na da hanu a kisan haka na nuna mana abin da muke tsammani dangane da gwamnatin kasar.
Kim Jon Nam dan shekara 45 ya mutu a ranar 13 ga watan Fabrairu bayan wasu mata su biyu sun shafa masa dafi a filin jirgin sama na Kuala Lumpur dake Malaysiya.
Jami’an 'yan sanda na Malaysia sun bayyana a ranar juma’a da ta gabata cewa dafin da akai amfani da shi wajen kashe Kim sunan sa VX Nerve Agent a turance, wanda an haramta amfani da shi karkashin dokar makamai masu Sinadari.
Facebook Forum