Firaministan kasar Spain Mariono Rajoy ya fadi jiya Asabar cewa zai fa rusa gwamnatin Catalonia mai ra'ayin aware ya kuma bayar da umurnin gudanar da zabe, a wani hanzari na hana wannan yanki mai 'yar kwarya-kwayar 'yancin cin gashin kai yin shelar ayyana cikakken 'yancinta.
Rajoy ya yi wannan sanarwar ce, bayan wani taron gaggawa na Majalisar Zartaswa jiya Asabar, kan yadda za a bullo ma wannan dambarwar siyasar, wadda ta biyo bayan matakan da shugabannin yankin na Catalonia su ka dauka na ballewa.
Tun ran Alhamis gwamnatin Spain ta dau matakin shafarar fage, na soke 'yar kwarya-kwaryar 'yancin cin gashin kan Catalonia saboda tsayawa kai da fata da Shugaban yankin ya yi na kama hanyar ayyana cikakken 'yancin kai.
Facebook Forum