Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ko Macedoniya Zata Sauya Suna A Yau?


Macedonia na zaben sauya suna

Shugaban Macedonia Gjorge Ivanov yayi kira ga yan kasar da su kauracewa zabar sabon sunan.

Al’ummar Mecedonia na kada kuri’a a yau Lahadi kan ko kasar zata sauya suna.

An bukaci yan kasar da sauya sunan kasar su zuwa Macedonia ta Arewa domin kawo karshen ja’in jar da akwa kwashe shekaru masu yawa anayi da makwabciyar kasar Greece, domin share hanyar shigar kasar cikin kungiyar NATO da tarayyar Turai.

Greece ta ce sunan Macedonia mallakin yankin Arewa ne kacokan, wanda amfani da sunan ya nuna niyyar Skopjes na mallakar yankin na Greece.

Tsawon shekaru Greece ta rika takura Skopje da ta sauya sunan kasar, inda ta matsa mata lamba da ta rika amfani da wani sunan na tsohuwar jamhuriyar Yugoslavia ta Macedonia a Majalisar Dinkin Duniya.

Haka kuma ta cigaba da hana karamar makociyar kasar daga samun damar zama mamba a NATO da kuma Tarayyar Turai indai har ta zauna da sunan.

Shugaban kasar Gjorge Ivanov yace yarda da bukatar Greece cin zarafin akidar kasane.”

Facebook Forum

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG