Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ko Yaya Gurbatacciyar Iska Ta Ke? Yaya Ta Ke Illa?


Ibrahim K Garba
Ibrahim K Garba

Yayin da kungiyoyi da daidaikun masu ruwa da tsaki ke ta kururuwa game da karuwar dumamar yanayi da kuma gurbacewar muhalli, hankalin jama'a da dama ya fara raja'a kan neman sanin ko mene ne ma gurbatacciyar iska da kuma illolinta. Malam Mainasara Nasarawa Funtua na daya daga cikinsu,

Yau za a ji amsoshin Mainasara Nasarawa Funtua, wanda ya yi tambayoyi kamar haka: “Ko yaya gurbatacciyar iska ta ke? Na ji masana sun yi hasashen cewa gurbatacciyar iskar za ta ninka har sau 30 nan da shekarar 2030. Shin mene ne illar gurbatacciyar iskar ga bil’adama?

To idan Malam Mainasara Nasarawa Funtua na saurare, ga cikakken Shirin Amsoshin Tambayoyinku na wannan satin mai dauke da amsar da wakilinmu a Adamawa, Salisu Mohammad Garba, ya samo ma ka daga Furfesa Sadik Futy na Sashin Ilimin Jografiyya a Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, Jihar Adamawan Najeriya, kamar haka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:12:27 0:00


XS
SM
MD
LG