Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KoreaTa Arewa Da Takwaranta Na Kudu Zasu Tattauna


North Korea leader with rockets and kids
North Korea leader with rockets and kids

Koriya ta Arewa da KOriya ta gudu zasu gana akan batun wasan Olympic dama batun dangantakarsu.Abinda sguhaban Amurka Donald Trump ke cewa yana fata batrun ya wuce na Olympic.

Shugaban Amurka Donald Trump yace yana fata tattaunawar da za ayi tsakanin koriya ta arewa data kudu ya zarta batun gasar wasan Olympics.

Yace yana fata Amurka zata shigo cikin wannan tattaunawar adai-dai lokacin da ya kamata.

Trump yayi wannan furucin ne a taron manema labarai da yayi da’yan jarida a wurin hutawar shugaban kasa dake Camp David inda ya gana da ‘yan majilisar dokoki na jamiyyar Republican.

Yace yana fata ganawar da akeyi tsakanin Seoul da Pyongyang zai cimma nasara.

‘Yace fata na shine inga cewa wannan tattaunaar ya wuce batun Olympic kana muma mu shigo a lokacin da ya dace.

Shugaba Trump yace ganin yadda abubuwa ke tafiya tsakanin kasashen koriyan guda biyu, to muddin wani abin azo a gani ya fito daga sakamakon taron wannan zai taimaka kwarai da gaske ga zamantakewa dama al’ummar duniya baki daya.

Yace yayi magana da shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-In kuma ya gode masa na matakin da yake dauka mai karfin gaske.

Yace tilas nekana shugaba ka rika rufe ido kana daukan waasu matakai kuma ni a kullun a shirye nake na dauki ire-iren wadannan matakan,domin irin su ne yasa tilasta Korea ta Arewa ta zauna da ‘yar uwanta.

Kwanan nan ne dai akayi musayan bakaken maganganu tsanin Shugaba Trump da shugaban na Korea ta arewa.

Wannan ne ma yasa shugaban na Korea ta Arewa yake cewa yana da naurar da zai latsa a bisa teburin sa da zai tarwatsa wasu sassan Amurka.

Wanda shimma nan take Trump ya mayar masa da martani a shafin na Twitter cewa a samu wani ya fada masa,nima ina da irin sa wanda ma yafi nashi kuma mai aiki bana wasan yara,ba don haka harttara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG