Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korea Ta Arewa Ta Jaddada Gwajin Makamin Nukiliyan Da Ta Yi


Shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Il da dansa Kim Jong Un, a cikin wannan hoton da kamfanin dillancin labarai na Koriya ya fitar ranar laraba 6 ga watan Oktoba. 2010,

Korea ta Arewa ta tabbatar da rahotannin cewa motsin kasa da aka ji da safiyar yau jumma’a a cibiyar gwajin nukiliyarta da ke Punggye-ri, gwaji ne na makamin nukiliya.

Wata sanarwar da aka bayar a gidan telebijin na kasar ta ambaci Cibiyar Binciken Makamin Nukiliya ta kasar tana tabbatar da samun nasarar gwajin nukiliya da aka yi domin tantance yadda za a iya hada kundun nukiliyar da za a iya aza shi kan makamai masu linzami.

Mai karanta sanarwar ya ce gwajin makamin nukiliyar, wani bangare ne na martani ga barazana daga Amurka da sauran abokan gaba da ke yin ko oho da matsayin Koriya ta Arewa a zaman wadda ta mallaki nukiliya.

Hukumomi a Pyongyang basu sanar da duniya aniyarsu ta yin gwajin kafin su gudanar da shi ba.

Wannan rana ta 9 ga watan Satumba ita ce ranar cikar shekaru 68 da kafa kasar Koriya ta Arewa, kuma a can baya, kasar ta kan gudanar da gwaje gwajen nukiliya ko na makamai masu linzami a muhimman ranaku irin wannan.

Kasashen duniya sun yi tur da wannan gwajin, wanda aka ce shine mafi karfi na nukiliya da Koriya ta Arewa ta taba gudanarwa.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG