Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korea Ta Arewa Ta Yi Gwajin Makami Mai Tafiyar Dogon Zango


Wani hoton talbijin ya na nuna yadda Korea ta arewa ta yi gwajin makamin roka mai tafiyar dogon zango
Wani hoton talbijin ya na nuna yadda Korea ta arewa ta yi gwajin makamin roka mai tafiyar dogon zango

Korea ta arewa, ta harba wani makamin roka mai tafiyar dogon zango a yau Lahadi, wanda ta kwatanta a matsayin aiki ne na harba na’urar tauraron dan adam.

Majalisar Dinkin Duniya ta haramtawa Korea ta Arewa amfani da fasahar makami mai linzami.

Da sanyin safiyar yau Korean ta yi gwajin a tashar Tongchang-ri da ke kusa da arewa maso yammacin kan iyakar kasar China.

Makamin dai ya nausa ne zuwa kudu maso yammaci, inda ya ketara ta saman tsibirin Okinawa da ke kasar Japan.

Daga baya Korean ta fitar da wata sanarwa ta kamfanin dillancin labaran kasarta, inda ta tabbatar da harba makamin rokan.

Wata rundunar sojin Amurka ta musamman ta ce ta ga gilmawar wani makami mai linzami a sararin samaniya, wanda ta ce an yi nasarar harba shi.

China da ta yi nuni da cewa wannan gwajin makamin ka iya zafafa zaman dardar din da ake ke yi a yankin.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG