Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta Arewa Da ta Kudu Suna Kai Wa Juna Ziyara Gab Da Wasannin Olympics


Hyon Song Wol shugabar kungiyar mawaka daga Koriya ta Arewa yayinda take Koriya ta Kudu
Hyon Song Wol shugabar kungiyar mawaka daga Koriya ta Arewa yayinda take Koriya ta Kudu

Wasanin Olympic na hunturu da za'a yi a Koriya ta Kudu sun zama sanadiyar tattaunawa da makwafciyarta Koriya ta Arewa da a can baya basa ko ga maciji tsakaninsu saboda yanzu sun soma ziyarar juna gabanin fara wasannin

Korea ta Arewa da makwabciyarta ta Kudu, suna kai wa juna ziyara, yayin da aka doshi gasar wasannin Olympics a Korea ta kudun, yayin da bangarorin biyu da ba sa ga-maciji, ke ci gaba da tattaunawa kan yadda Korea ta Arewan za ta shiga karbar bakuncin gasar wasannin na Olympics.

Wata tawaga daga Korea ta Kudu, ta kai ziyara arewaci a yau Talata inda za ta kwashe kwanaki uku, domin yin dubi kan yadda za a zabi wuraren da za a karbi bakuncin gasar a Birnin Pyongyang, ziyarar da ita ce ta farko cikin shekaru biyu.

Ziyara har ila yau na zuwa ne, kwana guda bayan da wata tawaga daga Korea ta Arewa, ta je Kudu, wacce ta samu jagorancin shugabar fitacciyar kungiyar mawakan nan ta mata da ake Moranbong Girl Band, domin su ga wuraren da za a karbi bakuncin gasar a Birnin Seoul.

A karkashin matsayar da bangarorin biyu suka cimma tsakanin Pyongyang da Seoul, kasashen biyu za su yi maci a karkashin tuta guda a ranar 9 ga watan Fabrairu da za bude gasar, sannan za su hada tawaga guda ta kungiyar mata ta ‘yan wasan kokara na Hockey.

Sannan kasashen biyu sun amince za su hada tawaga guda a wani wasan gargajiya da za a yi a tsaunin da ake kira Mount Kumgang da ke Korea ta Arewa

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG