Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Kara Gwajin Wasu Makamai Masu Linzami


A jiya Alhamis ne Koriya ta Arewa ta harba wasu makaman gwaji masu linzami da ke ci gajeren zango, wanda hakan ya nuna tsantsar rashin da’a ga takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba mata aka kuma rattaba masa hannu ba tare da bayyana sunan kowa ba cibiyar sulhu ta Majalisar Dinkin Duniyar.

Ma’aikatar Tsaron Koriya ta Kudu sun ce za su binciki lamarin. Har yanzu dai ba tabbacin rokoki nawa aka cilla, ko kuma masu cin gajere ko dogon zango ne ba. Amma ma’aikatar tace, wadannan rokokin da aka harba sun ci akalla nisan zango 100 zuwa 150 kafin suka fada a gabashin tekun Japan.

Wannan abun ban haushi dam aba sabon al’amarin bane daga Koriya ta Arewar, wacce ta sabo kalubalantar siyasar duniya game da al’amura ta hanyar nuna man hajar soji maimakon ta hanyar diflomasiyya.

Majalissar Dinkin Duniya da amincewa fiye da kasashe 50 suka amince da hukunta Koriya din game da gwajin makaminta mai linzamin da ke cin dogon zango, hukuncin da Amurka da China suka hada kai don zartar da shi.

XS
SM
MD
LG