Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Bayar Da Umurnin Cigaba Da Tsare Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya


Shugaban Tarayyar Nijeriya Goodluck Joanthan
Shugaban Tarayyar Nijeriya Goodluck Joanthan

Kotu ta bayar da umurnin cigaba da taare tsohon kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya mai fuskantar tuhuma kan zargin al'mundahana..

Kotu ta bayar da umurnin cigaba da taare tsohon kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya mai fuskantar tuhuma kan zargin al'mundahana.

Babbar Kotun Tarayya a babban birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja ta umurci Hukumar Yaki Da Almundahahana Da Dukiyar Al'umma (EFCC) ta cigaba da tsare tsohon kakakin Majalisar Dokokin Nijeriya Dimeji Bankole, har zuwa ran 10 ga wata, ranar da za a saurari bukatar neman belinsa

Hukumar Yaki Da Almundahana Da Dukiyar Al'umma ta ce a bayanan tuhumce-tuhumcen har 16 da masu shigabar da kara su ka gabatar an zargi tsohon kakakin Majalisa Dimeji Bankole da al'mundahanar kudi dala miliyan 60 mallakin Majalisar Wakilan Nijeriya. Tuhumce-tuhumcen sun hada da zargin hada baki a kara farashin komputoci da na'urorin wallafa da akwatunan talabijin. An kuma zarge shi da yin coge don samin damar sayan motocin alatu.

Hukumar ta ce an tuhumi tsohon kakakin Majalisar Wakilan ne don a cigaba da tsare shi kafin a kammala harhada bayanan sauran tuhumce-tuhumcen da ake masa.

Ran Lahadi da yamma ne dai Hukumar Yaki Da Al'mundahana Da Dukiyar Al'umma ta damke tsohon kakakin Majalisar Wakilan bayan turjiya ta sa'o'i hudu a gidansa da ke Abuja.

Hukumar ta ce ta damke tsohon kakakin Majalisar Dokokin ne bayan ta sami wasu bayanan sirrin da ke nuna cewa yana shirin sulalewa.

Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Nijeriya din dai ya karyata dukkannin zarge-zarge 16 da ake masa din.

XS
SM
MD
LG