Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Duniya

Kotu Ta Samu Trump Da Laifin Cin Zarafin Wata Mata Ta Hanyar Neman Yin Lalata


Tsohon hoto: Tsohon shugaban Amurka
Tsohon hoto: Tsohon shugaban Amurka

Kotu ta umurci Tsohon shugaban Amurka Donald ya biya matar da aka tabbatar ya yi ci zarafinta ta hanyar neman yin lalata da ita shekaru da dama da suka wuce, lamarin da Trump ya sha musantawa a baya.

Wata babbar kotu da ke zama a birnin New York a ranar Talata, ta umurci Trump ya biya wata mai ba da shawarwari a wata mujalla dalar Amurka Miliyan biyar ($5,000,000) bayan kammala sauraren bahasi da suka tabbatar da Trump ya aikata laifin cin zarafin matar ta hanyar yin lalata da ita shekaru 20 kafin ya zama shugaban kasa.

Masu shari’a su tara da suka hada da maza 6 mata 3, sun yanke wannan hukuncin ne bayan shafe sa’a' uku suna shawara, wannan shi ne karo na farko da Trump zai fuskanci tuhumar da aka same shi da laifi bayan kwashe shekaru yana fuskantar tuhume-tuhume daga matan da suke zargin shi da yin lalata da su.

TRUMP-ACUSACIONES-VISTAZO
TRUMP-ACUSACIONES-VISTAZO

Masu shari’ar sun yi watsi da zargin da E. Jean Carroll wacce yanzu take da shekaru 79 cewa, kan cewa Trump ya yi lalata da ita a dakin canza kaya na wani katafaren shagon sai da kaya a New York a shekarar 1996.

Amma kuma, sun yanke cewa ya ci zarafinta kana suka umurceshi da biyanta dalar Amurka miliyan 2 akan wannan zargin.

Sun kuma umurce shi da biyan Carroll dalar Amurka miliyan biyar a dalilin Trump ya yi ta musa tuhumar da ta yi mishi ta kafaar sada zumunta.

Trump
Trump

Daga bisani, Caroll ta fitar da wata sanarwa inda ta ce, “na shigar da karar Trump ne domin na wanke kainaa kuma na ceto mutunci na. Yau dai gaskiya ta yi halinta kuma duniya ta san gaskiyar lamarin. Wannan ba nasara ta ba ce ni kadai amma nasarar kowace macen da ta fuskanci wani cin zarafi a hannun Trump ne kana a ka ki yarda da ita.

Trump dai ya ce shari'ar bita da kullin siyasa ne, yana mai cewa sam bai san matar ba.

XS
SM
MD
LG