Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayoyi Sun Banbanta Kan Wanke Bukola Saraki Da Kotu Tayi.


Bukola Saraki.

Ra’ayoyi sun sha bam-bam tsakanin wakilan majalisa tarayyar dangane da wanke shugaban majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki.

Ra’ayi ya sha bam-bam tsakanin wakilan majalisa tarayyar dangane da wanke shugaban majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki.

A makon nan ne kotun da’a wacce take sauraron karar da gwamnatin tarayya ta shigar kan shugaban majalisar dattijan na kin bayyana dukiya ko kadaroinsa ta wanke shi.

Mai magana da yawun majalisar dattijai Senata Sabbi Abdullahi yace “Allah Ya wanke bawansa, amma wadanda tun farko suka hakikance cewa, Bukola yana da laifi ba zasu daddara ba.

A nasa bangaren Suleiman Nazif, ya bayyana farin cikin wannan hukunci, yana mai cewa, suna yiwa “Allah godiya”. Kuma suna tare da shugaban na su dari bisa dari.

Sai dai dan majalisar wakilai Hamma Isa Misau yace, tun fara shari’ar ya hangi cewa akwai matsala, domin akwai alamar karya aka kwantarawa senata Saraki.

Amma Ahmed Babba Kaita, yace akwai bukatar a sake nazarin yadda ake tafiyar da harkokin shari’a, ta yadda za’a gudanar da adalci, maimakon karkata hukunci saboda mukamin mutum

Wani dan jam’iyyar APC, mai mulkin kasar, Khalid Isma’il, yayi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya binciki bangaren shari’a saboda tabbatar da adalci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG