Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yankewa Dan Shah Rukh Khan Hukuncin Kwana 14 A Gidan Yari


Shah Rukh Khan
Shah Rukh Khan

Dan shekara 23, Aryan Khan, shi ne babban dan Shah Rukh Khan, fitaccen jarumi a masana'antar shirya fina-finai ta Bollywood a India.

Wata kotun Mumbai a India ta yankewa Aryan Khan, da ga jarumin Bollywood Shah Rukh Khan, hukuncin zaman gidan yari na tsawon kwana 14.

An yake masa hukuncin ne bayan da aka same shi da laifin mallakar miyagun kwayoyin tare da wasu mutan bakwai a wajen wani shagali da suka shirya a irin jirgin ruwan nan na alfarma.

A ranar Asabar aka kama Khan da mutanen bayan da aka kai samame cikin jirgin ruwan na alfarma a can gefen gabar tekun birnin Mumbai a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

Shekarun Aryan Khan 23, shi ne kuma babban dan tauraron na Bollywood.

Aryan Khan (a tsakiya) yayin da ake dauke da su a motar 'yan sanda
Aryan Khan (a tsakiya) yayin da ake dauke da su a motar 'yan sanda

An tsare shi ne bisa tsarin shari’a da zai kasance karkashin kulawar kotu maimakon hukumar da ke kula da ayyukan gyara hali.

Dan shekara 55, Shah Rukh Khan na daya daga cikin fitattun jarumai a duniya, wanda ake wa lakabi da “King of Bollywood,” wato “Sarkin Bollywood.”

Ya kwashe kusan shekara 30 yana wasan kwaikwayo a dandalin shirya fim na Bollywood inda ya fito a fina-finai sama da 105.

Shah Rukh na da mabiya sama da miliyan 42 a shafin Twitter, shi ne kuma mamallakin kungiyar wasan kulki ta cricket da ake kira “Knight Riders” da ke buga wasa a gasar Indian Premier League – gasar wasan cricket da ta fi armashi a duniya.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG