Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yi Watsi Da Zargin "Toronto" Da Ake Ma Bindow


Wasu lauyoyi a kotu
Wasu lauyoyi a kotu

Gwamna Mohammed Jibrilla Bindow na jahar Adamawa ya samu sa'ida a kalla a halin yanzu, bayan da wata kotun tarayya da ke Birnin Tarayya, Abuja ta yi fatali da kararsa da aka yi cewa ya mallaki takardun kammala makaranta na bogi. Amma da zauran zance.

Wata Babbar Kotu a Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja ta yi watsi da karar da wata kungiya ta yi ta bukatar a hana gwamna Mohammed Jibrilla Bindow na jahar Adamawa sake tsayawa takara bisa zargin cewa wasu takardun shaidar kammala makaranta da gwamnan ke amfani da su na bogi ne.

Da ya ke yanke hukunci, mai shari'a Adeniyi ya ce kotun ba ta ma da hurumin sauraren wannan karar tunda wanda ake zargi da mallakar takardun jabun ba a yakin Abujan ya ke ba.

To amma baya ga wannan kara da wata kungiya, daya daga cikin 'yan takarar gwamnan jahar Adawa karkashin jam'iyyar APC ta su Bindow mai suna Dr. Mahmud Hailu Ahmad, shi ma ya shigar da kara makamanciyar wannan. Wato dai da sauran rina a kaba ga gwamnan Bindow.

Ga dai Ibrahim Abdul'aziz da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:50 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG