Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa-Wata Kotu Ta Daure Mataimakin Shugaban Equitorial Guinea Saboda Zarmiya.


Teodoro Nguema Obiang Mangue, mataimakin shugaban kasa, da kotun Faransa ta yiwa daurin gyara-halinka.
Teodoro Nguema Obiang Mangue, mataimakin shugaban kasa, da kotun Faransa ta yiwa daurin gyara-halinka.

KUngiyoyin yaki da cin hanci da rashawa Transparency International da Sharpa ne suka shigar da kararrakin kan kasashen Afirka uku.

A Faransa wata kotun kasar jiya Jumma'a ta daure mataimakin shugaban kasar Equitorial Guinea Teodorin Obiang, daurin shekaru uku wanda ba zai zauna a gidan fursina ba, watau daurin jeka ka gyara-halinka, saboda satar dukiyar jama'ar kasar da kuma badda sawunsu, inda ya sayi gidaje da kadarori a faransa. Toedorin Obinag shine dan shugaban kasar E/Guinea Teodoro Obinag.

Haka nan kotun ta shi tarar dala milyan 35 wanda shima ba sai ya biya ba. Haka nan kotun ta bada umarnin akwace dukkan gidaje da kadarorinsa dake kasar. Mallakar san sun hada da wani gini mai dakuna dari, da wani gida wanda kundisa dala milyan 123 kusa da fitacciyar unguwar da ake kira Champs Elysse, da kasar ta Equitorial gini ta ce ginin na jakadanci ne.

Wannan shari'a, itace irin ta farko da kungiyoyi da suke yaki da cin hanci da rashawa watau Transparency Interantional da wata da ake kira Sharpa suka shigar kan shugabannin kasashen Congo-Brazaville, da Gabon, da Equitorial Guinea, ind a suke zargin su da cin amana, d satar dukiyar al'umar kasashen domin biyan bukatun kansu.

Lauyan daya daga cikin kungiyoyin ya gayawa Sashen Faransa na MA cewa wannan hukunci yayi dai dai domin ya aike da sako shugabannin sai rai yayi halinsa, da manyan jami'an gwamnati da kuma bankuna cewa su shiga taitayinsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG