Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Soke Hukuncin Da Ya Halalta Zubar Da Juna Biyu A Amurka


Masu goyon bayan soke hukuncin da ya halalta zubar da ciki suna murna a Amurka
Masu goyon bayan soke hukuncin da ya halalta zubar da ciki suna murna a Amurka

Da ma dai an jima ana tsammanin wannan matsaya da kotun ta dauka ta soke dokar da ta ba mata damar zubar da ciki wacce aka kwashe shekaru 50 ana amfani da ita

Kotun kolin Amurka ta yi watsi da hukuncin nan da ya ba da ‘yancin zubar da juna biyu, wanda aka fi sani da Roe v. Wade.

Hakan na nufin yanzu za a bar jihohi da zabin haramtawa ko akasin haka.

Da ma dai an jima ana tsammanin wannan matsaya da kotun ta dauka ta soke dokar da ta ba mata damar zubar da ciki wacce aka kwashe shekaru 50 ana amfani da ita.

Wannan hukunci da kotun mai rinjayen masu ra’ayin mazan jiya ta yanke a ranar Juma’a, na zuwa ne kasa da watanni biyu bayan da aka kwarmata wani kuduri da kotun ke shirin amince wa da shi, wanda ya shafi wannan hukunci na na batun zubar da ciki.

Yayin da kotun ta sauya hukuncin Roe v. Wade da ake kwatance da shi a batun wannan takaddama, wanda aka yanke a 1973, wata shari’a da ake yi da kungiyar tsarin iyali ta Planned Parenthood da Casey, ba ta haramta zubar da juna biyun ba, sai dai tasirin hukuncin kotun kolin, zai yadu zuwa sassan Amurka kamar wutar daji.

Har ila yau wannan matsaya da kotun ta dauka inda alkalai 6 suka amince yayin da uku suka nuna adawa, na faruwa ne a wata shari’a ta daban da ake yi a kan dokar jihar Mississippi da ta haramta zubar da juna biyu bayan ya kai tsawon makonni 15.

XS
SM
MD
LG