Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Amurka Ya Amince da Hana Wasu Mallakar Bindigogi


Loretta Lynch Sakatariyar Ma'aikatar Shari'ar Amurka kuma Antoni Janar din kasar

Hukuncin na jiya Litini, mai rinjayen alkalai 6 akasin 2, wata nasara ce ga masu son ganin an takaice wanzuwar bindiga, wadanda su ka kara azama bayan munanan harbe-harben da aka yi a wata mashakatar dare dake Orlando, jihar Florida.

Shari'ar ta shafi wasu mutane biyu da su ka bugi abokan zamansu, don haka aka same su da aikata kananan laifukan cikin gida a jihar Maine.

Wata dokar tarayya, ta haramta ma duk wanda aka same shi da irin wannan laifin, mallakar bindiga.

To amma mutanen sun ce wannan bai shafe su ba, saboda sun bugi abokan zaman nasu ne lokacin da ake cikin tashin hankali, su ka kasa hakuri amma ba da gangan ba.

Kotun dai ta yi watsi da wannan hanzarin, ta ce fassarar Majalisar Tarayya game da kananan laifuka, ba ta tsame laifin da aka aikata cikin rashin hakuri ba.

"Duk mutumin da ya bugi wani cikin rashin hakuri, ya yi amfani da karfinsa, kuma bai gaza wanda ya aikata hakan da gangan ko manufa ba," a cewar bayanin alkalai mafiya rinjaye da Mai Shari'a Elana Kagan ta rubuta.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG