Accessibility links

Kotun Kolin Kasar Kenya Ta Tabbatar Da Zaben Uhuru Kenyatta

  • Grace Alheri Abdu

Zaman Kotun Kolin Kasar Kenya
Kotun kolin kasar Kenya ta yanke hukumci yau asabar inda ta tabbatar da sahihancin, sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar 4 ga watan Maris da cewa Uhuru Kenyatta shine ya lashe zaben.

Hukumcin da kotun ta yanke yau ya biyo bayan karar da aka shigar kotu da ya tada hankalin kasar. Yanke wannan hukumcin na nuni da cewa, za a rantsar da Kenyatta watan gobe a matsayin shugaban kasa.

Hukumar zaben kasar Kenya tace Uhuru Kenyatta ya lashe zaben da sama da kashi hamsin bisa dari na kuri’u. sai dai abokin hamayyarsa Raila Odinga yace an sauya sakamakon wadansu mazabu.

Wadansu kungiyoyi kuma sun ce hukumar zaben ta sanar da sakamakon zabe tun kafin ta kamala kirga kuri’u.

Hukumcin da kotun kolin ta yanke cewa ba a bukatar gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar zai kwantar da hankalin al’ummar kasar Kenya da suke fargaban yiwuwar shida tashin hankali.
XS
SM
MD
LG