Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Laberiya Zai Saurari Bangaorin Majalisar Biyu Akan Kakakinsu


Shugabar Liberia Johnson Sirleaf

A yau Litinin, wata kotu a Liberia, za ta saurari bangarori biyu da ke takaddama da juna a majalisar wakilan kasar.

Kusan ‘yan majalisu 40 daga cikin 73, na neman Kakakin Majalisar, Alex Tyler, ya sauka daga mukaminsa, yayin da ya ke fuskantar tuhuma kan zargin karbar cin hanci.

Wani mai taimakawa alkali a sauraren shari’a, ya zargi Tyler da wasu jami’an gwamnati da wani dan kasuwar da wani kamfanin kasar waje mai hakar ma’adinai, da hanu a wannan badakala, kamar yadda wani rahoton kungiyar nan da ake kira Global Witness mai hedkwata a London ta fitar a rahotonta.

Kungiyar ta Global Witness, ta bayyana cewa kamfanin kasar wajen, ya biya manyan jami’an gwamnati sama da dala dubu Dari tara da hamsin, domin mallakar wani filin hakar ma’adinai a shekarar 2010.

Rahoton ya yi zargin cewa Tyler ya karbi dala dubu saba’in da biyar a matsayin kudin tuntuba.

Sai dai Tyler na zargi shugaba Ellen Johson Sirleaf da hanu a kokarin da ake yi ganin an tsige shi daga mukaminsa.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG