Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Nijar Ta Wanke Mutumin Da Ake Zargi Da Aibanta Alkalai a Shafin Facebook


Muhammadou Issoufou, shugaban Jamhuriyar Nijar
Muhammadou Issoufou, shugaban Jamhuriyar Nijar

A karshen watan da ya gabata jami’an tsaro suka kama Gamaci Muhammad na kawancen kungiyoyin masu fafituka, bayan da aka zareg shi da shiga shafin Facebook ya muzanta wasu alkalan kasar, lamarin da ya sa hukumomi suka tsare shi.

Wata kotu a birnin Yamai dake Jamhuriyar Nijar ta sallami wani mai gwagwarmaya bayan da ya shafe makwanni uku a tsare a gidan yari saboda zarginsa da aka yi da yi wa alkalai kazafin cin hanci ta hanyar shafin facebook.

A karshen watan jiya hukumomin kasar suka cafke Gamaci Muhammad.

“Shi dai Gamaci an ce dukkan abinda ake tuhumarshi ba laifi ba ne, ba gaskiya ba ne, saboda haka kotu ta ce daga yau an wanke shi.” In ji lauyansa.

Ba sabon abu bane a kasashe masu tasowa musamman ma a Afirka, a ga hukumomi suna fito-na-fito da masu shiga shafin Facebook suna sukarsu.

A daya bangare kuma kotu har ila yau, ta yanke wa wani dan adawa hukuncin zaman wakafi saboda samin sa da laifin cin zarafin mashara’anta a shafin sada zumunta, hukuncin da lauyansa ya ce za su daukaka kara.

Ana zargi Ibrahim Banakasa, kusa a jam’iayr Modem Lumana mai adawa da laifin shiga shafin Facebook ya soki wani hukuncin wata kotu, wanda aka ce ka iya tasiri akan hukuncin da alkalin zai yanke nan gaba a shari'ar.

An yanke mai hukuncin zaman gidan yari na tsawon watannin uku, inda zai kwashe watanni biyu a waje sannan ya kuma yi wata daya a gidan yari.

Tuni Banakasa ya kwashe makwannin uku ya zuwa yanzu, ya rage masa mako guda kenan.

Saurari rahoton wakilin Muryar AMurka Sule Mumuni Barma domin jin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG