Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Rasha Ta Ki Bada Belin Paul Whelan


Wata Kotun a Rasha ta ki bada belin wani ba-Amurke da ake zarginsa da laifin leken asiri.

Paul Whelan, wanda ke zaman dan kasashen Amurka da Biritaniya, tsohon soja ruwa a Amurka ne da aka kama shi ran 28 ga watan Disamaba bayan da hukumar tsaron kasar Rasha ta zarge shi da laifin leken asirin kasa, koda yake kuma hukumomin Rasha din ba su bayyana ainihin laifin da ake zarginsa da aikatawa ba.

Iyalansa sun ce ba shi da wani alifi.

Mutumin dan shekaru 48 ya bayyana a kotu a birnin Moscow a yau Talata, yana neman a sake shi, amma alkalin ya ki amincewa da hakan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG