Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Amince Gwamnati Ta Rike Kudaden Diezani


Tsohuwar Ministar Man Fetur din Najeriya Alison Madueke
Tsohuwar Ministar Man Fetur din Najeriya Alison Madueke

Biyo bayan karar da hukumar EFCC ta shigar yanzu wata kotun Legas ta tabbatarwa gwamnatin tarayyar Najeriya mallakar kudaden da aka gano tsohuwar ministar man fetur Alison Madueke ta wawure

Ranar 9 ga wannan watan ne Justice Chuka Obiozo na kotun tarayya dake Legas ya zartas da hukumci na wucin gadi da ya mallakawa gwamnatin tarayya makudan kudaden da aka gano su cikin bankin Stirlin.

Hukumcin alkalin ya biyo karar da hukumar EFCC ta shigar ne. A hukumcin farko alkalin ya umurci bakin ko kuma ita ministar ko wanda ya san ya mallaki kudin ya gurfana a gaban kotun tare da sheidu cikin makonni biyu. Sai dai bayan makonni biyu babu wanda ya je kotun saboda haka kotun ta mallakawa gwamnati kudaden na dindindin

Ita hukumar EFCC ta tabbatarwa kotun cewa kudaden mallakar tsohuwar Minista Alison Madueke ne da aka kyautata zaton ta wawuresu ne daga hukumar matatar man fetur ta kasa NNPC a shekarar 2014.

Hukumar EFCC ta zargi tsohuwar ministar da ajiye kudaden a bankuna guda uku. Sai dai tun a watan Fabrarirun bara alkali Musiliu Hassan na kotun tarayya ya amince da karbe kudaden dake sauran bankunan guda biyu.

Kudaden da kotun ta mallakawa gwamnatin tarayya sun hada da N23.4bn da wasu N9bn.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG