Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kristoci Sun Fara Gudanar Da Bukukuwan Easter a Fadin Duniya


Yadda Kiristoci Suka Gudanar Da Bukukuwan Easter A Jihar Kano

A yau Juma’a mabiya addinin kirista a fadin duniya ke gudanar da bukukuwan Easter, don tunawa da mutuwa da tashin Isa Almasihu.

A ranar Juma’ar Easter, mabiya addinin kirista sun yi imani da cewa rana ce da aka kashe Yesu Almasihu, wanda tashinsa daga matatattu ya kasance sanadin ceto daga hallaka da kuma alkawarin rayuwa na har abada da kaucewa shiga wutar jahannama ga duk wanda yayi imani da Isa Almasihu.

Rabaran Bakari Ibrahim ya ce Easter na cikin ginshikan koyarwa da abin da mabiya addinin kirista suka fi bada fifiko a kansa.

Mabiya addinin Kirista a fadin duniya kan gudanar da bikin Easter daga ranar Juma’a zuwa Litinin, kuma sau daya a kowacce shekara domin tunawa da mutuwa da tashin Yesu Almasihu, sai dai ba wai suna bikin rana ko lokacin da ya mutu bane.

Madam Lami Ibrahim dake koyarwa a cibiyar tauhidi a birnin Jos ta ce Easter na da muhimmanci sosai a rayuwar kirista.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Facebook Forum

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG