Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ku Taya Ni Murna, Wakar “Da Ma” Ta Samu Masu Kallo Miliyan Daya – Namenj


Namenj (Instagram/ Shafin Namenj)
Namenj (Instagram/ Shafin Namenj)

Ba dai kasafai ake samun wakokin Hausa suna samun masu kallo kamar haka a shafin YouTube cikin dan kankanin lokaci ba kamar yadda bincike ya nuna.

Wakar “Da Ma” wacce mawakin Hausa Namenj ya rera, ta samu adadin mutum miliyan daya da suka kalli wakar a shafin YouTube.

Ya samu wannan adadi ne cikin wata biyu bayan da ya sake ta a kusan tsakiyar watan Maris din bana.

“Ku taya ni murna, “Da Ma” ta samu masu kallo miliyan daya a YouTube. Sai da ku masoya. Na gode maku.” Namenj ya rubuta a shafinsa na Instagram.

Hakan na nufin cikin kasa da wata biyu kenan ya samu adadin wadanda suka kalli wakar.

Ba dai kasafai ake samun wakokin Hausa suna samun masu kallo kamar haka a shafin YouTube cikin dan kankanin lokaci ba kamar yadda bincike ya nuna.

Namenj, wanda na daya daga cikin matasan mawakan Hausa da tauraronsu ke haskawa, ya rera wakar ne tare da gayyato takwaran sana’arsa Hamisu Breaker.

Breaker, wanda shi ma fitaccen mawakin Hausa ne da ya samu karbuwa, shi ya rera wakar “Jaruma.”

Namenj wanda a baya ya yi wakar “Fatana” wacce ya sake a watan Fabrairun da ya gabata, ya fito idon duniya ne bayan da ya dauki salon kwaikwayon wakokin fitattun mawaka har da na kudancin Najeriya da ma na kasashen waje.

Ya maimaita wakokin fitattun mawaka kamar Ali Jita da wasu wakokin da aka yi a wasu fina-finan Hausa.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG