Accessibility links

Kudancin Sudan Ta Yi Watsi Da Zargin Sudan Cewa Tana Marawa 'Yan Tawayen Arewaci Baya

  • Aliyu Imam

Wata mummunar fashewa kusa da ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kudancin Kordofon.

Gwamnatin kudancin Sudan tayi watsi da zargin da Sudan tayi mata cewar tana goyon bayan‘yan tawayen da Sudan ke fafata rikici dasu a kan iyakokin kasashen biyu.

Gwamnatin kudancin Sudan tayi watsi da zargin da Sudan tayi mata cewar tana goyon bayan‘yan tawayen da Sudan ke fafata rikici dasu a kan iyakokin kasashen biyu.

Sanarwar da ta fito daga Ma’aikatar harkokin wajen Kudancin Sudan jiya laraba na cewa babu kanshin gaskiya a zargin na kasar Sudan cewar Kudancin Sudan na goyon bayan mayakan ‘yan tawaye dake jihar kudancin Kordofon.

Kudancin Sudan tace rikicin da Sudan ke fama dashi nada nasaba ne da matsalar bambancin dake akwai tsakanin jam’iyyar dake mulkin Sudan da jam’iyyar SPLM a Kudancin Sudan, matsalaar da ta biyo bayan sakamakon zaben da aka gudanar shekarar da ta gabata.

XS
SM
MD
LG