Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar FEMA za ta Kare 'Yan Gudun Hijira da Kuma FCT


Shugaban Hukumar FEMA Mallam Abbas Iddris na duba yadda ake rabon kayan tallafi.

Hukumar Tallafin Gaggawa Ta Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja (FEMA) ta ce ya zuwa yanzu akwai akalla 'yan gudun hijira sama da 4,000 da ta ke kula da su. Kuma za ta tabbatar cewa miyagu basu saje da su sun addabi jama'a ba.

Shugaban Hukumar Agajin Gaggawa ta Birnin Tarayyar Najeriya Abuja da Kewaye (FEMA), Alhaji Abbas Iddris, ya ce hukumar na daukar matakan ganin cewa mugaye ba su saje da ‘yan gudun hijira na hakika don cutar da jama’a ba.

A wata hirar da abokin aikinmu Yusuf Aliyu Harande ya yi da shi a yau dinnan a birnin Washington, Shugaban na hukumar FEMA ya ce tuni Ministan Birnin Tarayyar Najeriya Abuja, Senata Bala Muhammad (Kauran Bauchi) ya ba da umurnin kafa kwamiti na tantance ‘yan gudun hijirar da su ka fito daga arewa maso gabashin Najeriya don tallafa masu. Ya ce ‘yan kwamitin sun hada da jami’an tsaro da wasu hukumomin gwamnatin da abin ya shafa. Ya ce kodayake tuni aka dan ba ‘yan gudun hijirar dan abin hasafi, da zarar an warware zare da abawa dangane da su za a tallafa masu sosai.

Ya ce a yanzu haka adadin ‘yan gudun hijirar ya zarce 4,000 kuma ana duban yadda za a tsugunar da su na dindindin. Za a ga yadda za a maida masu sana’a kan sana’o’insu. Amma ana bai wa kowannensu dan abin lallaba rayuwa na wuccin gadi kafin a kammala tantance su.

Alhaji Abbas ya ce hukumar ta FEMA da jihohin da ‘yan gudun hijnirar su ka fito na tuntubar juna don sanin halin da ake ciki a jihohin. Kuma da zarar zaman lafiya da kwanciyar hankali sun kankama a jihohin, to ‘yan gudun hijirar za su koma wurarensu.

Alhaji Abbas ya ce a yanzu kira su ke ga sauran hukumomin da ke da alaka da batun ‘yan gudun hijirar da su hada kai da hukumar ta FEMA don agaza ma ‘yan gudun hijirar. Ya ce su a hukumar ta FEMA ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen taimakon ‘yan gudun hijirar da kuma kare Birnin Tarayyar Najeriya Abuja daga miyagu duk iya karfinsu.

Hukumar FEMA za ta Kare 'Yan Gudun Hijira da Kuma FCT - 4'21"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:21 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG