Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kumbon Curiosity Ya Sauka Sumul Kan Duniyar Mars


Kumbon Curiosity
Kumbon Curiosity

Kumbon Curiosity ya sauka daidai inda aka auna shi a bayan da ya shafe watanni 8 yana tafiyar kilomita miliyan 566 kafin ya isa Mars

Jiya litnin Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, NASA, ta yi bukin murnar sauka sumul da wani kumbonta yayi a kan duniyar Mars, ta kuma fara nazarin hotunan farko da ya turo nan duniya.

Injiniyoyi a dakin harba kumbo na Hukumar NASA sun yi ta sumbatar juna su na tsalle su na tafi da murna a bayan da kumbon ya aiko da sako daga sararin samaniya cewa ya samu sauka salun alun ta cikin iskar dake kewaye da Mars, matakin da shi ne mafi wuya a wannan yunkurin binciken ko akwai wani abu da yayi kama da halitta a wannan curin kasa.

Kumbon mai suna Curiosity, wanda dakin binciken kimiyya ne wanda girmansa ya kai karamar mota, ya sauka daidai inda aka auna shi a ranar lahadi, a bayan da ya shafe watanni takwas yana wannan tafiya mai nisan kilomita miliyan 566.

Hotunan farko da kumbon ya aiko masu launin fari da baki, sun nuna doron kasar Mars inda ya sauka da garawul, da wani dutse can nesa daidai rana tana kokarin faduwa da kuma hanyar da kumbon ya biyo ta cikin saman duniyar ya sauka a doronta.

Na’urorin kumbon Curiosity masu aiki da karfin nukiliya, zasu shafe shekaru biyu su na bincike da tabe-tabe da sunsuno ko an taba samun wata halitta a kan duniyar, ko kuma akwai abubuwan da zasu iya kyale halitta ta rayu a kan wannan curin jar kasa, wadda daga nan duniya ake hango ta kamar tauraruwa.
XS
SM
MD
LG