Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kunar Bakinn Wake Ya Halaka Mutane 26 Tare Da Jikata Wasu Da Dama


Wurin da 'yan kunar bakin wake suka kai hari yau Litinin a Bagadaza

Ana kyautata zaton kungiyar ISIS ce da aka tarwatsa daga wasu sassan kasar Iraqi ta kai wani sabon hari a birnin Bagadaza wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 26 tare da jikata wasu da dama

Wasu ‘yan kunar bakin wake biyu sun tarwatsa kawunansu a babban birnin Iraqi a yau Litinin, suka kashe mutane akalla 26 da raunana wasu da dama.

Bama-baman sun tarwatse ne a dandalin Tayran dake tsakiyar birnin Bagadza a lokacin cunkoson masu zuwa aiki da safiya. Wannan wurin cibiyar hada hadar kasuwanci ne, kuma akwai leburori dake taruwa don neman aiki.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan hari amman hare haren da suka gabata can baya dai kungiyar ISIS ce suka kai su.

Kungiyar ta mamaye mafi yawan sassan arewaci da yammacin Iraqi na tsawon shekaru fiye da uku.

Harin da Sojojin Iraqi tare da hadin gwuiwar Amurka suka rika kaiwa ta sama ne ya taimaka wajen korar kungiyar ta ISIS daga manyan biranen kasar da wasu sassan da ta mamaye.

A watan da ya gabata ne Firayim Minista kasar Haider Al-Abadi, ya bayyana nasarar fatattakar mayakan kungiyar daga wuraren da suka kama, amma kuma har yanzu ana fuskantar hare-haren ‘yan ta’addan a sassa dabam dabam na Iraqi.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG