Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kunar bakin waken Somaliya: Ana samin karin gawarwaki


Cigaba da neman mafita a rikice-rikicen Somaliya

Ana ci gaba da samun yawan adadin mutanen da suka rasa rayukansu da jikkata a dalilin harin kunar bakin waken da aka kaiwa wani sansanin soja da mayakan rundunar sojin tarayyar Afirka keda zama a Somaliya.

Ana ci gaba da samun yawan adadin mutanen da suka rasa rayukansu da jikkata a dalilin harin kunar bakin waken da aka kaiwa wani sansanin soja da mayakan rundunar sojin tarayyar Afirka keda zama a Somaliya.

Jami’ai a Somaliya sun bayyana cewar wani dan harin kunar bakin wake ne ya cika mota da boma-bomai ya doshi kofar shiga sansanin sojan sannan ya tada boma-boman a dab da shiga kofar sansanin dake garin Afgoye mai tazarar kilomita talatin daga birnin Mogadishu a yau Asabar. Jami’an tsaron kasar Somaliya sun fara gudanar da binciken afkuwar kai harin.

Idan za’a tuna a watan jiya ne sojin tarayyar Afirka suka baiwa sojin Somaliya cikakken kai harin hadin gwiwar da suka sami nasarar korar mayakan al-shabab daga tunggarsu dake yankin Afgoye.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG