Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar al-Shabab Ta Kashe Wata 'Yar Jarida A Somaliya


Masu goyon bayan kungiya al-Shabab suna zanga zanga
Masu goyon bayan kungiya al-Shabab suna zanga zanga

A can kasar Somaliya , jiya Lahadi aka harbe wata 'yar jarida mai suna Sagal Salad Osman a birnin Mogadishu, wadda take yiwa gidan rediyon talibijan na kasar.

Babban sakataren kungiyar 'yan jarida ta kasar Somaliya Mohammed Ibrahim Moalimu ya fadawa Muryar Amurka cewa wasu 'yanbindiga da ba'a san ko su wanene ba suka harbe Sagal a gundumar Hodan a lokacin da take barin wata jami'a.

Yace nan da na yan bindigan suka arce daga wurin.

Sagal Osman itace 'yar jarida mace ta biyu da aka kashe a kasar Somaliya cikin watanni shida da suka shige.

A watan Disamban shekara ta dubu biyu da goma sha biyar aka kashe wata 'yar jarida mai suna Hindi Hajj Muhammad a sakamakon wani hari da aka kai da wani bam da aka boye cikin wata mota.

Kungiyar Al Shabab tayi ikirarin cewa ita ke da alhakin kai harin

XS
SM
MD
LG