WASHINGTON, DC —
Koch na kungiyar kwallon kafar Arsenal, yace sayo dan wasa ba abu ne me sauki ba kamar yadda ake gani.
Shugaban kungiyar Mr. Arsene Wenger a shirye yake don bude kofar saye da siyarwar yan wasa a watan Janairu, ya kuma yadada cewar dole yayi tunani wajen zabe.
Don ‘yan wasa masu rauni sunyi yawa a tawagar kungiyar ta Mr. Wenger, wanda dan wasa Mesut Ozil na fama da ciwon Guywa, Jack Wilshere na fama da idon kafa, Mikel Arteta na fama da ciwon kafa , Yaya Sanogo na fama da ciwo a cinyar shi, shi kuma Mathieu Debuchy na fama da ciwon idon kafa, da dai sauransu.
A kwai dai alamun kungiyar ta Arsenal nashirin motsi a watan Janairu, wanda take ta 8 a wasan firimiya Lig bayan rashin nasara na baya-da-baya.