Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Boko Haram Ta Kai Hari A Garin Pallam A cikin Jihar Adamawa


Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.
Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.

kungiyar Boko Haram ta kai hari a garin Pallem, kuma sun kashe mutane kana sun kone babban asibitin garin

‘Yan kungiyar boko haram sun kai hari a kauyen Pallam dake cikin karamar hukuma Madagali a jihar Adamawa,Sun kai wannan harin cikin dare ne.

kamar yadda rahotanni ke cewa sun bude wuta babu kakkautawa tare da kona gidaje,baya ga awon gaba da wasu da lamarin ya rutsa da su.

Wani mazaunin yankin da ya tsallake rijiya da baya,ya bayyana cewa an samu asarar rayuka tare da kona babban asibitin garin.

Wakilin Muryar Amurka Ibrahim AbdulAzeez yace har lokacin da yake hada rahoton, hukumomi a jihar basu ce kome ba game da wannan harin.

Sai dai Dan Majilisa Adamu Kamale dake wakiltan wannan yankin ya koka game da karancin jamian tsaro, yace wannan harin ba shine irin san a farko ba.

Ga Ibrahim Abdulazeez da Karin bayani.2’54

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG