Accessibility links

Kungiyar Boko Haram Tayi Alkawarin Daina Kaiwa Jami'an Tsaro Hari

  • Grace Alheri Abdu

Wakilan kungiyar Boko Haram ta Najeriya wadda Amurka ke yin gargadi game da yiwuwar wani harin da za ta kai kan manyan otel-otel din da Turawa ke sauka a Abuja.

Kungiyar Boko Haram tace daga yanzu ta daina kaiwa jami'an tsaro hari ta kuma nemi suma a daina kai masu hare hare

Mataimakin shugaban kungiyar Jamatu Lidda awati Ahli suunati wal Jihad wadda aka ba lakabi da sunan Boko Haram, Muhammad Marwana ya bayyana cewa kungiyar ta saki turawa yan kasar faransi guda bakwai da suka saka yi garkuwa da su na tsawon watanni biyu sabili da sa baki da kuma roko da al'ummar musulmi sukayi tayi a kafofin yada labarai da kuma nuna alamar zahiri dangane da batun neman sasantawa da gwamanatin Najeriya take nema.

A cikin hira da wakilinmu na jihar Bauchi, mataimakin shugaban kungiyar har ila yau yace daga yanzu kungiyar zata daina kai hari kan jami'an tsaro, ta kuma bukaci ganin suma jami'an tsaro su daina kai hare hare kan al'umma.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG