Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Jihar Adamawa Ta Tallafawa Makarantun Firamare da Kayayyaki


Barkindo Aliyu Mustapha Lamidon Adamawa

A sanadin illar da kungiyar Boko Haram ta yiwa makarantun jihohin Borno da Adamawa, Kungiyar Dillalan Man Fetur jihar Adamawa ta tashi domin ta taimaka da kayan aiki da makarantun ke bukata

A Najeriya , yayin da ake kokarin tada komadar makarantu da rikicin Boko Haram ya shafa a jihohin arewa maso gabas, yanzu haka Kungiyar Dillalan Man Fetur Masu Zaman Kansu wato IPMAN ta kaddamar da wata gidauniyar tallafawa Makarantun firamare da kayyakin karatu da kuma na kiwon lafiya.

Daman dai bincike ya nuna cewa a jihohin arewa maso gabas akwai makarantu da dama dake cikin ha’ula’I, masu matsananciyar bukatar tallafi a yanzu, duk da ikrarin da gwamnatocin jihohin ke yin a cewa suna nasu kokari.

Kayan tallafin da suka hada da magunguna, kujeru, wuraren zuba shara, da ma randunan ruwa na zamani, na zuwa ne yayin da ake kokarin tada komadar makarantu da rikicin Boko Haram ya shafa a jihohin arewa maso gabas.

A jihar Adamawa, daya daga cikin jihohin da rikicin na Boko Haram ya shafa, hadakar kungiyar dillalan man fetur ta ce daukan wannan mataki na cikin kokarin da kungiyar ta soma don hada karfi da karfe don kawo cigaban al’umma.

Tun farko da yake jawabi, mai martaba Lamidon Adamawa, Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa, wanda Dan Amar Adamawa kuma Hakimin Jimeta, Alhaji Muhammad Baba Paris ya wakilce shi, yace lokaci yayi da za’a daina dogaro da gwamnati akan kowane lamari.

Su ma malaman makarantun da aka baiwa agajin sun yaba ainun da wannan tallafin da suka samu.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG