Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ECOWAS na shirin kara takunkumi wa wa sojojin Mali


Dakaru na daukar matakan tsaro bayan juyin mulki a Mali
Dakaru na daukar matakan tsaro bayan juyin mulki a Mali

Kungiyar bunkasa dangantaka da cinikayya a tsakanin kasashen Afirka ta yamma (ECOWAS) tace tana shirin sake azawa shugabannin sojin kasar Mali takunkumi

Kungiyar bunkasa dangantaka da cinikayya a tsakanin kasashen Afirka ta yamma (ECOWAS) tace tana shirin sake azawa shugabannin sojin kasar Mali takunkumin hanasu sakewa idan har suka ci gaba da daukan matakan hana mika mulki hannun farar hula.

Yau litinin, ECOWAS ta fidda wata sanarwa dake la’antar matakan da jagoran shugabannin mulkin sojan Mali Kyaftin Amadou Sanogo da mukarrabansa ke ci gaba da dauka na yin shisshigi a ayyukan Gwamnatin rikon dake kunshe da farar hula zalla.

A zaman tattaunawar Asabar, saida jakadun ECOWAS biyu suka fice daga zauren taron saboda wani cece-kucen da aka rika yi tsakanin jakadun da jagoran mulkin sojan kan wanda yafi dacewa ya jagoranci Gwamnatin rikon.

Kwanaki 40 suka rage a wa’adin da aka baiwa jagoran Gwamnatin riko Dioncounda Traore domin kafa sabuwar Gwamnati, amma kuma jagoran sojin juyin mulki Kyaftin Sanogo na kokarin tilasta ganin shine zai zama sabon shugaban Gwamnatin rikon da za’a kafa. Hakan ya janyo hankalin darektan yada labarum ECOWAS Sonny Ugoh.

Yace za’a ci gaba da tattaunawar da ake yi, daman amfani tattaunawar ke nan idan an sami cikas sai a kokarta warware matsalar snanan aci gaba da tattaunawa har sai an kai ga samun nasarar cimma daidaituwa.

XS
SM
MD
LG