Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Fulani Ta Sha Alwashin Magance Rikicin Fulani Da Manoma.


Cudanyar Fulani da mutanen gari ta zama dole
Cudanyar Fulani da mutanen gari ta zama dole

Yayin da ake ta samun rigingimu tsakanin Fulani da manoma, wata kungiyar Fulani ta yi hobbasa wajen ganin abin ya zama tarihi

Sakamakon rikice-rikicen da ake samu tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma a kudancin jihar Taraba ta arewa maso gabashin Najeriya, yanzu haka shugabannin Fulani a jihar, sun ce sun dau matakan kawo karshen rigingimun.

Taron Fulanin, wanda aka yi karkashin kungiyar Fulani ta kasa da kasa ta Tabital Puulaku, ya yi zargin cewa da hannun wasu dake amfani da wadannan rikice-rikicen don cimma muradunsu, batun da suka ce a yanzu ba zasu sake amincewa ba.

Shugaban kungiyar a jahar Taraba, Bello Bamme Alhaji Nyame ya jaddada cewa sun hada kai da gwamnatin jahar ne saboda a san cewa ba su tare da wadanda ya ce sun a sato kayan mutane daga wasu jahohi sun a kawowa jahar. Shi ma Sarkin Fulanin Hardo-Kola, Alhaji Ali Jauro ya yi kira ga Fulani da manoma su ki yadda miyagu na hada su fada don amfanar kansu.

Ga wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz da rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG