Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar G5 Na Sahel Tace Zata Samar Da Ayyukan Yi Ga Matasa


Shugabannin Kungiyar G5 Sahel
Shugabannin Kungiyar G5 Sahel

Kungiyar G-5 a yankin Sahel tana gudanar da taro a jamhuriyar Niger, da zummar inganta matakan tsaro da samar da ayyukan yi ga matasan kasashen ta.

Kungiyar ta G5 Sahel, ta kunshi kasashe ne da suka hada da Mali, da Bukina Faso, da Niger da Chadi da kuma da Murtania.

Yanzu haka kungiyar tana gudanar da taron ta zagaye na hudu tun bayan da kasashen suka kafa rundunar hadin gwiwa da zummar yaki da kungiyoyin taaddancin da suka mamaye arewacin Mali, kuma suke kai hare-hare a kasashe makwabta irin su Nijar da Bukina Faso.

Taron wanda ake gudanarwa yau,yazo dai-dai da lokacin da shugaban ta na farko, shugaban kasar Mali Ibrahim Bubakar Keita, ke kammala waadin shugabancin sa na Kungiyar.

Daya daga cikn abinda taron na yau zai baiwa fifiko shine batun hada kai domin samun zaman lafiya da cigaban kasashen na yankin Sahel.

Shugaban na Mali yace haka kuma zasu ci gaba da karfafa ayyukan cigaban karkara, samar da aikin yi ga matasan kasashen su, da batun samar da makamashi.

Ga Sule Mumuni Barma da Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG