Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar G5 Sahel Ta Sake Lale A Yaki Da Ta'addanci


Taron Yan Majalissun Dokoki G5 Sahel A Kasar Niger.

Shugabanin Kungiyar G5 Sahel da na hadin guiwar kungiyoyin Alliance SAHEL sun gudanar da taro a Jamhuriyar Nijar a ci gaba da neman hanyoyin inganta rayuwar jama’ar yankunan da matsalar tsaro ta jefa cikin halin zaman dar- dar.

Sake maido da kyaukayawar rayuwa wa jama’ar yankunan da matsalar tsaro ta afkawa a kasashe 5 mambobin kungiyar G5 Sahel shine abinda gwamnatocin wadanan kasashe ke hange ta hanyar hadakar kungiyoyin Alliance Sahel mai huldar aiki da manyan kungiyoyin duniya. Dalili kenan da wadanan bangarori suka hadu a Yamai da nufin duba yiyuwar gagauta kaddamar da ayyukan da talakawa zasu gani a kasa.

A karkashin wata yarjejeniyar da bangarorin suka cimma masu hannu da shuni sun amince zasu bayarda kudaden tafiyar da ayyukan dake kunshe a tsarin inganta rayuwar jama’a yayinda kasashen G5 Sahel suka jaddada aniyar tabbatar da doka da oda don baiwa talakawa damar samun walwala a duk inda suke.

A watan Disanba dake tafe shugabanin kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso da Chad da Mauritania zasu gudanar da taron koli da zummar bibiya kan ayyukan da wannan taro ya bayarda shawara akansu, da kuma batun rundunar hadin guiwar G5 Sahel mai alhakin murkushe kungiyoyin ta’addancin da ke addabar jama’a akan iyakar Mali da makwaftanta.

Saurari Cikakken rahoton Souley Moumouni Barma

Taron kungiyar SAHEL-3:10"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG