Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Hammas Ta Kawo Karshen Rikicin Da Take Yi


Palestine - Senior Hamas leader Ismail Haniyeh speaks . UNDATED
Palestine - Senior Hamas leader Ismail Haniyeh speaks . UNDATED

Kungiyar Hammas mmai gwagwarmaya da makami tayi ba zata jiya lahadi domi ta dauki matakin kawo karsgen rikici da take yi a siyasance.

Jiya Lahadi kungiyar Hamas mai gwagwarmaya da makami ta dauki matakin kawo karshen rikicin da ta ke yi a siyasance da kuma kan mallakar yankin kasa da kungiyar Fatah ta Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas, inda Hamas ta amince ta rusa shugabancinta ta shiga babbar zabe.

Yayin da tattalin arkin Gaza ya ruguje ta yadda ma wutar lantarki ta tsawon sa'o'i hudu kawai ake samu a rana a wannan yankin kasa da ke gabar kogin Maditareiya, kungiyar ta Hamas ta ce za ta bar gwamnatin hadin kai da Abbas ke jagoranta ta karbi ragamar mulki yankin. Tun shekaru uku aka kafa gwamnatin ta hadin gwiwa to amma ta kasa iko da wajen sai a yanzu.

Wannan cigaban da aka samu ya biyo bayan tattaunawar da aka yi dabam-dabam tsakanin wakilan Hamas da Fatah da jami'in hukumar leken asirin Masar a birnin Alkhahira.

Wani jami'i kungiyar Hamas mai suna Hussam Badran ya ce hukumomin na Gaza sun amince da bukatar Abbas ta kawo karshen takaddamar da ke tsakanin kungiyoyin Falasdinawan biyu a matsayin abin da ya kira, "kyakkyawan fata dangane da shirin da ake yi na sasantawa. A yanzu haka an rusa kwamitin gudanarwar kuma don haka gwamnati na iya zuwa Gaza ta dau nauyin da ya rataya a wuyanta."

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG