Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Harin Bam A Masallacin Shi'a dake Kabul


Masallacin Baqir ul Olum na Shi'a inda harin ISIS ya kashe mutane 32 tare da jikata wasu 80 jiya Litinin

Duk da yakin da Iraqi da kawayenta keyi da kungiyar ISIS har yanzu kungiyar na kara kai hare hare na baya bayan nan shi ne wanda ta kai Kabul babban birnin Afghanisatan wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jikata wasu masu dimbin yawa

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin harin bam na kunar bakin wake da aka kai a wani masallacin ‘yan Shi’a dake Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, wanda mutane akalla 32 suka hallaka a cikinsa, wasu fiyeda 80 suka jikkata.

Rahottani sunce dan kunar bakin waken da ya kai harin ya shige cikin masallacin Baqir ul Olum ne, ya sade da sauran jama’a yayinda ake gudanarda wata hidimar ibada a cikin masallacin, sannan ya tada bam din dake makalle a jikinsa.

Babban Kwamandan hukumar Binciken laifukka ta Kabul, General Faridoon Obaidi, ya gayawa manema labarai cewa dukkan wadanda wannan harin ya shafa, fararen hula ne.

Tuni dai shugaban kasar ta Afghanistan, Asharaf Ghani, ya la’anci harin, wanda yace makiyan kasar tashi ne suka kawo shi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG